By Abbas Yakubu yaura
Tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Legas, Alhaja Sinatu Ojikutu, ta koka kan yadda hukumar wayar da kan jama’a ta kasa take yin kasa a gwiwa, inda tace ba ta yi wani abin da ya dace na wayar da kan jama’a ba.
Ojikutu ta bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin kaddamar da wani littafi mai suna, ‘Stain on Humanity’ a jihar Legas.
Littafin mai shafuka 164, wanda Kabir Bakare ya rubuta, ya kunshi babi 10 dake dauke da batutuwan da suka shafi wasu al’adun gargajiya masu cutarwa a Afirka, tsarin kabilanci, kyamar baki, kisan kare dangi, mulkin mallaka, bauta,nuna wariyar launin fata, da yaki da ‘yancin jama’a.
A wata hira data yi da wakilinmu, Ojikutu ta ce, “Za a iya kawar da matsalolin zamantakewar dake addabar kasar a halin yanzu ta hanyar kwakkwaran shawarar shugabanninmu da al’umma. Tsarin bayanai a Najeriya ya yi matukar wahala kuma ba a amfani da hukumar wayar da kan jama’a kamar yadda ya kamata don wayar da kan jama’a yadda za a yi al’amura.”
Bakare, yayin da yake magana game da littafinsa, yace, “Al’adar yin shiru ta yi tasiri wajen bayar da rahotanni kamar cin zarafin mata. Kamata ya yi a yi hukunci mai tsanani ga masu laifi kuma dole ne a tallafa wa wadanda abin ya shafa a hankali da tunani. Dole ne a sauya tsarin al’adu kuma gwamnati na da rawar da take takawa wajen bayar da shawarar wajen samun wannan sauyi.”