Hukumar kidaye ta kasa NPC ta tabbatar da cewa zata yi duk mai yiwuwa a aikin kidayar da zata gudanar a shekarar 2023, wajen ganin ba a samu wata matsala ba.
Shugaban hukumar ta NPC Alhaji Nasir Kwarrane ya bayyana hakan a Abuja, yayin kaddamar da shafin hukumar domin tattara bayanai, da kuma bangaren da ai kula da ayyukan da wakilansu zasu gudanar ta hanyar amfani da wayoyin su na hannu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa shafin hukumar an samar da shi ne domin tattarawa tare da adana bayanan da za a dinga dauka da zarar an fara aikin kidayar.
Wannan dai wani kokari ne da hukumar ke yi wajen ganin, ta yi amfani da hanyar zamani don zamanantar da tsarin baki daya, duba da yadda zamanin ya sauya ta fuskoki da dama.
Kwarra, wanda ya samu wakilcin Mrs Gloria Izonfuo wato kwamishinar kasa daga jihar Bayelsa, t ace kaddamar da shafin hukumar zai taimaka wajen saukaka shigar da bayanai da kuma adana su.
Daga nan sai ta tabbatar da kudurin hukumar na amfani da hanyar zamani, wajen gudanar da kidayar kuma tare da tabbatar da daidaiton da ya kamata don cin nasarar shirin.