By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar tsaro ta RRT, da hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, a jihar Taraba, a jiya sun kama wasu barayin wayoyin famfo guda biyu da suka yi barna a ranar jajibirin Kirsimeti.
Kwamandan NSCDC na jihar, Ugwuja Edwin, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Jalingo, babban birnin jihar yayin da yake gabatar da mutanen biyu tare da wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifin a hedikwatar hukumar.
Barayin sun sace igiyoyin wanda aka kwato su daga wajen su daga kamfanin samar da ruwa da magudanan ruwa na jihar Taraba TAWASCO, wanda ke samar da ruwan sha ga mazauna Jalingo da kewaye.
Kwamandan rundunar, Edwin, ya ce an kama su tare da kwato kebul din da ya kai na miliyoyin Naira tare da hadin gwiwar ‘yan banga.
Sannan ya ce a halin yanzu ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da wadanda suka yi barnar a gaban kuliya a lokacin daya dace.
Ya kuma bai wa mazauna jihar tabbacin cewa rundunar tana nan a tana iya bakin kokarinta wajen gadi sannan ya bukace su da su kwana da idanuwansu biyu.
Da yake mayar da martani game da kama wasu barayin ruwa guda biyu, Manajan Daraktan TAWASCO, Engr. Buba Siam, ya ce kamfanin samar da ruwa na fama da ‘yan fashi da makami, kuma ya yi farin ciki da wannan labari.
Ya ce kebul din da aka sace yana watsa ruwa zuwa famfon ruwa sannan kuma yana samar da ruwa ta bututun karkashin kasa ga al’ummar jihar.
Ya bukaci rundunar da su fadada aiyukan su domin tabbatar da cewa an kama gungun barayin ruwan da ke barazana ga harkokin kasuwancinsu.