Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC, reshen jihar Osun, ta kama wani matashi dan shekara 29 mai suna Abdulrahman Ibrahim da wata mota kirar Toyota Camry da ya sace.
Kwamandan NSCDC na Jihar Osun, Emmanuel Ocheja, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa an sace motar kirar 1999 mai lamba AGG 24 TC a yankin Oke-Oniti da ke Osogbo.
Ya ce mamallakin motar, Aderemi Akeem, ya shaidawa NSCDC a Osogbo cewa an sace motarsa kuma ya yi cikakken bayani ga jami’an, inda suka gudanar da bincike a kan lamarin.
Ocheja ya ce binciken ya kai jami’an NSCDC jihar Kano inda aka gano motar da aka sace daga Osogbo.
A hirarsa da majiyar Jaridar Dimokuradiyya, wanda ake zargin ya ce ya sayi motar ne a garin Ibadan na Jihar Oyo ya kai ta Kano ba tare da sanin cewa motar sata ba ce.