By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an tsaron farin kaya na Najeriya, NSCDC reshen jihar Kwara, sun kafa wata tawagar mata domin tabbatar da tsaro a makarantun dake fadin jihar.
Sabuwar rundunar da aka kafa an kafa ta ne domin magance matsalar sace ‘yan makaranta da ake yi a jihar.
Kwamandan NSCDC na jihar, Makinde Ayinla ne ya sanar da hakan a Ilorin, babban birnin jihar a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai ayyukan hukumar na shekarar 2021.
“Tawagar mata da zata rika sanya ido a makarantunmu don tantance daliban da aka sace za a bayyana a wannan watan.
“Mun horas da wasu zababbun ma’aikata akan haka kuma da izinin gwamnan jihar za mu tura su makarantu a wannan watan,” in ji Ayinla.
Kwamandan ya ce hukumar za ta yi maganin rashin tausayin da ake nunawa kan daliban a bana a kokarin da take yi na hana zagon kasa ga tattalin arzikin kasar da kuma kare gine-ginen gwamnati.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa hukumar ta NSCDC tace za ta hada kai da hukumar kwastam domin magance masu fasa kwauri a garuruwan kan iyaka dake fadin jihar.
Ayinla ya kuma yi tsokaci game da shirye-shiryen hukumar NSCDC na ci gaba da sanya ido na sa’o’i 24 a cibiyoyin gyaran hali don dakile duk wani abu na rashin tsaro a wuraren.
Kazalika ya ce hukumar za ta kara kaimi kan horar da jami’anta musamman a fannin sarrafa makamai da kuma tattara bayanan sirri domin kara taimakawa ayyukansu.
Ya bayyana cewa, sashin Agro-Ranger na hukumar, a shekarar 2021, ta gudanar da shari’o’i 76 kan harkokin noma da rikicin manoma da makiyaya, inda ya kara da cewa an warware 63 daga cikin kararrakin.