Jami’an Hukumar Tsaron Fararan Hula da kaddarorin Gwamnatin NSCDC shiyar jihar Anambra sun cafke mutane hudu da ake zargi da saffarar lita 90,000 na gurbataccen Mai da a cikin manyan motoci guda biyu, a kan babbar hanyar Onitsha zuwa Owerri a garin Ihiala na jihar..
Kwamandan hukumar NSCDC a jihar Everestus Obiyo ne ya bayyana hakan a jiya Talata, yayin da yake ganawa da manema labarai a jihar.
Obiyo ya ce bincike ya nuna cewa, wadanda ake zargin ba su da lasisin sarrafa man fetur, yayin da manyan motocin da ake amfani da su ba su da izinin dakon Mai.
Ya Kara da cewa, wadanda ake zargin duk sun furta matsayinsu daban -daban a cikin laifukan, kuma ana ci gaba da bincike, bayan haka za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu da zaran ankammala.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun kai hari a aAbia sun lalata gidage
Kazalika ya bayyana sunayen wadanda ake zargi kamar haka; Mohammed Nuradden Mai shekara 30, Sani Zubaru Mai shekara 43, Abdulahi Lawal Mai shekara 3, da kuma Suleman Mohammed Mai shekara 36 dukkannin su sunfitone daga jihar Kaduna.