By Abbas Yakubu Yaura
Jami’an hukumar yaki da fataucin bil-Adama da hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC) a jihar Akwa Ibom sun damke wani Elisha Effiong da yunkurin sayar da ‘ya’yansa mata guda biyu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Effiong, wanda ya hada baki da matarsa domin cefanar da ‘ya’yan nasu mata guda biyu masu shekaru shida da kuma mai shekaru hudu domin biyansa basussukan da ake bin sa, an kama shi ne a Uyo a ranar 15 ga watan Nuwamba.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC, Umana Ukeme, a wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, ya ruwaito wanda ake zargin yace ya yanke shawarar sayar da ‘ya’yansa ne sakamakon matsananciyar wahalar daya ke sha.
Sannan an ce wanda ake zargin ya amince da wani jami’in tsaron sirri na tsare-tsarensa, yayin da mai gadin ya sanar da kwamandan NSCDC, Mista Abidemi Majekodunmi inda suka gudanar da bincike kan lamarin har ta kai gano tare da kama wanda ake zargin.