Hukumar kula da Fararan hula da tsaron kadarorin gwamnatin reshen jihar Kebbi ta nisanta Kanta da sanarwar da ake yanawa a kafofin sada zumunta na zamani dake cewa, ta gargadi al’umar jihar nan, da su kauracewa bin hanyar Dakingari zuwa Bunza saboda an hango alamun yan bindiga a hanyoyin dake yankunan.
Lokacin da yake Karyata rahoton Kakakin hukumar na jihar Kebbi DSC Akeem Babatunde Adeyemi ya bayyana cewa, sakon ba daga shelkwatar hukumar yake ba.
A cewarsa, tuni hukumar ta Civil Defence ta fara gudanar da bincike domin zakulo wadanda ke da hannu a yada irin wannan labarin na kanzon kuregen, da kuma danganta shi ga hukumar reshen jihar Kebbi, don hukunta su domin kaucewa afkuwar hakan a gaba.
A wani labarin Kuma na daban.
Jami’ar BUK, ta umurci dukkanin daliban da ke zaune a harabar jami’a guda biyu da su bar dakunan kwanan dalibai da daukacin harabar jami’ar a ranar 20 ga watan Maris ko kuma kafin ranar 20 ga watan Maris.
Jami’ar ta kuma dakatar da shirin ayyukan ta a harabar da aka fara tun da farko har sai an dawo da cikakken ayyukan ilimi.
Wata sanarwa da sakataren yada labarai na jami’ar Bala Abdullahi ya fitar a madadin magatakardar jami’ar, ta bayyana cewa matakin da hukumar ta dauka ya biyo bayan tsawaita yajin aikin gargadi da kungiyar malaman jami’oi ta ASUU ta yi na yajin aikin watanni biyu.
Sannan sanarwar ta kara da cewa “Daga ranar da aka ce hukumar za ta dakatar da bayar da dukkan taimakon na ayyukan ta ga dakunan kwanan dalibai.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa an dauki matakan ne don “kare duk wani laifin da ba’a zata ba da kuma sakamakon da zai biyo baya.”
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Hukumar Gudanarwar Jami’ar Ibadan (UI), ta rufe cibiyar, inda ta umarci dukkan daliban da su fice daga dakin kwanan daliban da ke cikin makarantar ba tare da bata lokaci ba.
Idan dai ba’a manta ba jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a wa’adin farko na yajin aikin da kungiyar ta ASUU ta tafi ya haifar da zanga-zanga a sassa daban daban na kasar inda daliban suka nuna rashin amincewar su kan yajin aikin da kungiyar ta ASUU ta keyi.
Kazalika daliban da suka gudanar da zanga-zangar sunyi zargin gazawar ministan ilimi wajen kasa cimma matsaya tsakanin sa da kungiyar ta malam jami’oi ASUU inda wasu daga cikin kungiyoyin dalibai suka bukaci ministan da yayi murabus daga mukamin sa.