By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar ‘yan sanda ta tura ma’aikata kasa da guda 380 don sanya ido kan gwajin masu neman aikin ‘yan sanda da zai gudana a fadin kasar a ranakun juma’a da Asabar masu zuwa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kimanin ‘yan sanda 10,000 ne za a daukesu aikin a lokacin atisayen.
Hukumar ta PSC ta yi alkawarin tabbatar da ingancin jarabawar cancantar da aka yi wa ‘yan takara, inda ta yi nuni da cewa duk wani ma’aikaci ko dan sanda da aka samu da laifin yin hakan za a hukunta shi.
Da yake jawabi ga ma’aikatan hukumar yayin wani shirin wayar da kan jama’a na kwana daya a Abuja, ranar Laraba, babban sakatare dindindin da kuma sakataren hukumar, Mista William Alo ya umarce su da su gudanar da kansu cikin mutunci da mutunta ka’idojin dake jagorantar jarabawar.
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na PSC, Ikechukwu Ani,ya fitar mai taken, ‘Dole ne mu tabbatar da ingancin aikin daukar ma’aikata -PSC,Alo ya ce ya yi farin ciki da kyakkyawar alakar dake tsakanin hukumar ta PSC da rundunar ‘yan sandan Najeriya. sannan ya umurci ma’aikatan su yi aiki tare da jami’an ‘yan sanda a cibiyoyin jarrabawar.
A cewarsa, halinsu zai yi magana mai kyau ko mara kyau ga hukumar kuma za mu hukunta duk wani ma’aikacin da ya kawo wa hukumar abin dariya da gangan, inda ya kara da cewa hukumar za ta tabbatar da nasarar aikin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar ta tura ma’aikatanta zuwa cibiyoyin jarabawa daban-daban na jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya domin gudanar da jarabawar tare da ba da umarnin tabbatar da ingancin aikin.
Kazalika“Hukumar ta ba da shawarar cewa ya kamata a ba da rahoton wasu laifuka ko kuma zagon kasa ga atisayen ta hanyar layukan wayar data samar kamar haka 07080601377 ko 07080601376 domin daukar mataki cikin gaggawa.”