Dr Chioma Ejikeme, Sakatariyar gudanarwa na Hukumar lura da fansho wato PTAD ta bayyana gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wacce ta fi kowanne aminci ga ‘yan fansho a tarihin Nijeriya.
Ejikeme ta bayyana hakan ne a ranar Juma’a a garin Jos a yayin tantance ‘yan fanshon da suka fito daga jihohin Arewa ta tsakiya.
A cewarta, gwamnatin ta magance dukkanin matsalolin da ‘yan fanshon suke fuskanta a kasarnan, inda ta kara da cewa; magance matsalolin ya sanya ‘yan fansho sun yi farin ciki da gwamnatin har suka bai wa shugaban aminci.
Babbar Sakatariyar gudanarwar, ta tabbatarwa da ‘yan Fanshon da aka rike musu hakkokinsu cewa; da zarar kudi sun samu, za a biya su dukkkanin hakkokinsu.