Daga: Wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
A yanzu haka dai Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta baza komar ta wajen neman wani Furodusa wanda ya shirya wani fim na Badala mai suna Labaran Duniya, wanda tuni ya fara tayar da kura, tun daga lokacin da aka fara saka wani yanki na fim din a kafar sadarwar Social Media da sunan talla.
Fim din dai yana nuni tare da koyar da harkar Badala tsakanin maza da maza da Kuma tsakanin Mata da Mata. Kan haka ne yasa mutane da suka ga tallan suka rinka yin tofin Allah tsine da Kuma Allah wadai ga masu shirya fim din.
A Bincike da Jaridar Dimokuradiyya ta gudanar ya tabbatar mata da cewar fim din an dauke shi ne a Jihar Jigawa, Amma daga Kano aka je can aka shirya fim din don gudun matakin da Hukumar tace fina-finai za ta dauka a Kan masu shirya fim din.Sai dai duk da haka a yanzu Hukumar tace fina-finan ta baza komar ta wajen nema tare da kamo wanda ya shirya fim din domin daukar mataki na shari’a a Kan sa.
Shugaban Hukumar tace finafinai ta jihar Kano Malam Ismail Na’abba Afakallahu ya fadawa wakilinmu cewa.
“Ba za mu bari a ci gaba da shirya fina-finai masu bata tarbiyyar mu ba don haka duk inda masu shirya fim din su ke sai mun nemo su tare da kamo su domin daukar matakin Shari’a a Kan su. Domin mun sani wasu ne su ke daure musu gindi don ganin wannan Hukumar ba ta yi nasara ba a wajen aikin da take yi na kawo gyara a harkar shirya fina-finan da a ke yi ba.
Kazalika ya kara da cewa don haka mu a shirye muke mu dauki dukkan matakin da ya dace don ganin mun kawo gyara wajen gyara tarbiyyar Jama’ar jihar mu da ma kasa baki daya.
Daga karshe Afakallahu ya yi Kira ga Jama’a da su ci gaba da bai wa Hukumar sa goyon baya don ganin an samar da fina-finan da suka dace da addinin mu da kuma al’adar mu.