By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar tara haraji ta jihar Gombe ta bankado wata kungiyar mutane biyar dake fitar da sanarwar bukatu a cikin hukumar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a ranar Asabar, Shugaban Hukumar, Abubakar Tata, ya yi alkawarin gano tushen lamarin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wannan dai ba shi ne karon farko da hukumar ke bankado irin wadannan munanan ayyuka ba. Ko a shekarar 2019, wasu ma’aikatan hukumar tara kudaden shiga sun sace kimanin rasitar biyan kudin lantarki guda 10,000.
Tata Yace hakan ya biyo bayan bankado masu biyan harajin ne domin tantance masu aikata laifin a cikin ma’aikatar, inda ya kara da cewa ana yin yawa don ganin an samu hayyaci da kuma ganin a kawar da muggan kwai.
A cewar Tata, ’yan kungiyar biyar da suka amsa laifin an kama su ne biyo bayan yunkurin yin jabun sa hannun babban daraktan dake kula da ayyukan haraji na jihar.
Yayin da yake shawartar masu biyan haraji da ka da su biya tsabar kudi ga duk wani jami’in tattatara kudaden shiga ko haraji da ba zai ba su takardar shedar biya ba mai dauke da sunan mai biyan haraji da lambar wayar ba,sannan ya bada tabbacin cewa ma’aikatan dake karkashinsa na yin iya kokarinsu wajen tsaftace tsarin.
Ya kara da cewa, ‘’Yan kungiyar biyar wadanda suka yi jabun sa hannun babban daraktan dake kula da ayyukan haraji sun amsa laifin sahannu daban-daban kuma an basu takardar ladaftarwar aiki har zuwa lokacin da hukumar za ta mika martaninsu ga kwamitin ladabtarwa.