By Ishaq Dabai
Hukumar tsaftace muhalli ta jihar Legas tace ta kwace babura 410 dake bin hanyoyin da aka haramta a cikin jihar a cikin mako guda.
Shugaban hukumar, CSP Shola Jejeloye, ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Mista Femi Moliki, ya fitar ranar Alhamis.
Jejeloye ya ce hukumar ta yanke shawarar baza ta huta a kan bakar ta ba har sai an daina yin watsi da dokokin zirga zirgar ababen hawa da babura ke yi a cikin birnin.
Yace an kwace babura 300 a kan hanyoyin da aka haramta daga ranar 13 ga Satumba zuwa 17 ga Satumba, yayin da aka kama 110 a ranar Laraba.
Shugaban ya ce jami’an hukumar sun aiwatar da aikin a yankin Isolo, Ojodu Berger, Ojota, Island Island. Jejeloye yace ci gaba da saba dokokin hanya da masu babura keyi a Legas abin damuwa ne.
Ya kuma bukaci mazauna Legas da su guji bada goyon bayan masu babura da ke bin manyan hanyoyi, tare da tabbatar da cewa “ya fi kyau a zauna lafiya fiye da nadama”.