By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC), ta sanar da lokacin da za a fitar da sakamakon jarabawar kammala makarantun sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) na ‘yan takara masu zaman kansu na shekarar 2021 zango na biyu
Hukamar WAEC ta bayyana cewa za a fitar da sakamakon a yau Litinin, 14 ga watan Fabrairu, 2022.
WASSCE ‘yan takara masu zaman kansu kuma wandand aka fi sani da Babbar Jarrabawar Takaddun shaida, GCE, an rubuta su a cikin watan Nuwamba zuwa Disambar shekarar data gabata.
Jarabawa wacce ta kasance mai zaman kanta wacce kuma bata buƙatar yunifom, amma yin rajistar biometric ya zama dole.
Galibi daliban da suka kammala sakandare ne suke daukar jarrabawar da suke son gyara kurakuran sakamakonsu.
WAEC, a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Lahadi da daddare, ta rubuta cewa: “@waecnigeria za ta sanar da fitar da sakamakon WASSCE na ‘yan takara masu zaman kansu na shekarar 2021-zango na biyu a gobe Litinin 14 ga watan Fabrairu, 2022. Ku kasance da mu domin jin karin bayani.”