Gwamnan Jahar Gombe Muhammadu Yahaya ya amince da naɗa Olanre Daniel a matsayin Shugaban Hukumar Wasanni ta Jahar Gombe nan take.
Sakataren Gwamnatin Jahar Farfesa Ibrahim Njodi wanda ya sanar da naɗin Gwamnan, yace matakin ya biyo bayan ajiye muƙami da Shugaban Hukumar yayi Hamza Soye.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yajin Aikin ASUU ya taɓa ɗiyan Ngige — Ministan Ƙwadago ya gayawa Ƙungiyar Ɗalibai
Soye, a cikin takardar daya aike wa Gwamnan a ranar Talata, ta hanyar Sakataren Gwamnatin Jahar ya bayyana sauka daga mukamin.
Idan dai za’a tuna a wani taro, Gwamnan yasha alwashin ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa na bada Naira Miliyan 20 duk wata.
A lokacin da aka tuntuɓe shi, Soye yace yayi gaggawa yayi magana.