Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumar za ta bukaci Naira biliyan 305 domin gudanar da zabukan 2023.
Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa a zauren majalisar a ranar Litinin.
Shugaban na INEC ya kuma lura da cewa adadin zai baiwa hukumar damar shirya zaben da kuma siyan duk kayan zaben da ake bukata da kuma gudanar da zabukan fidda gwani a fadin kasar nan.
Sai dai ya bayyana cewa tuni hukumar ta karbi Naira biliyan 100 daga cikin kudaden da ake bukata na zaben.
A halin da ake ciki, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da kasafin kudi Sanata Jibrin Barau, ya bayyana cewa za a gabatar da kasafin kudin shekarar 2022, a yi muhawara, sannan a zartar da shi a ranar Talata 21 ga watan Disamba.
Kazalika, babu wani bayani kan ko shugaba Buhari ya rubuta kuma ya mikawa majalisar dokokin kasar wasika kan matakin da ya dauka na bada ko janye kudurin sa na yin kwaskwarima ga dokar zabe.
Wa’adin kwanaki 30 da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade ga shugaban kasa ya mayar da martani kan kudirin ya kare ne a ranar Lahadi 19 ga watan Disamba.
A halin da ake ciki, majalisar dokokin kasar za ta fara hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara daga ranar Talata 21 ga watan Disamba.