Hukumar zabe ta kasa mai Zaman kanta INEC ta tabbatar da nasarar Dan takarar PDP Bello Matawalle, a matsayin Wanda ya lashe zaben gwamna a zamfara.
Mahmoud Yakubu, shugaban INEC ne ya sanar da haka yau a Abuja inda yace Jam’iyyar ta lashe duk kujerun jahar.
Yakubu, yace bayan samun nasara da PDP tayi, ita kuma Jam’iyyar APC an soke duk kujerun su da kuma duk ‘yan takarkarun su na apc .
Matawalle ya samu kuri’a 189,452 inda ya zama shine na biyu a zaben Gwamna.