Hukumar dake kula da babban birnin tarayya Abuja ta dawo da dokar hana amfani da babura na kasuwanci wato Okada.
Daily Post ta ruwaito cewa, Don haka, ta kame babura 75 saboda karya doka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Yankewa Masu Damfara Ta Yanar Gizo 66 Hukunci A Ibadan
Ikharo Attah, babban mataimaki na musamman kan sa ido, dubawa da tabbatar da tsaro ga ministan babban birnin tarayya Abuja, shine ya jagoranci tawagar da suka gudanar da aikin a ranar Talata, a mahadar Dutse-Alhaji, mahadar Larabawa, Jahi da Kubwa Phase 4.
Ya ce an aiwatar da dokar ne kai tsaye bisa ga umarnin Ministan ga manyan sassan gudanar da mulki don kawar da babura na kasuwanci a birnin.
Attah ya kuma yi nuni da cewa za a ci gaba da gudanar da wannan aiki, inda ya ce ya zama wajibi ne a yi hakan, biyo bayan ayyukan rashin da’a da masu tuka mashin na kasuwanci ke yi a wuraren da bai kamata su yi aiki ba.
Ya bayyana cewa tun da aka fara aikin, rahoton da aka tabbatar daga Kubwa a fannin tsaro, ya nuna cewa an samu nasara kashi 11 cikin 100.
A cewar sa, a hankali za a kawo karshen barazanar da ake fuskanta sanadiyar ayyukan yan okada a yankin.
A WANI LABARI KUMA: Sojoji Sun Kubutar Da Uwa Da ‘Ya’yanta A Kaduna
Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun ceto wata uwa da aka yi garkuwa da ‘ya’yanta hudu tare da wasu mutanen kauyen uku a wani sintiri a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun.
Daily Trust ta ruwaito cewa sojojin sun fuskanci luguden wuta daga ‘yan bindigar a lokacin da suke sintiri a kan titin Birnin Gwari-Gyam-Kuriga-Manini.