Jami’an tsaro sun yi wa Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba da suka kai hari a wata cibiyar gyaran hali da ke Jos babban birnin jihar Filato kofar Rago a harabar gidan.
DAILY POST ta ruwaito cewa wasu ’yan ta’adda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki cibiyar ce, a yammacin jiya Lahadin dauke da muggan makamai kuma suna ta harbe-harbe a harabar cibiyar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar gidan yari ta Najeriya NCoS, CC Francis Enobore ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun fada tarkon jami’an tsaro ne bayan wani musayan wuta da suka yi a tsakanin su, inda nan take jami’an tsaro suka killace farfajiyar gidan gyaran halin.
Sanarwar ta ce; “Cibiyar gyaran hali da ke Jos, Jihar Filato ta fuskanci harin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa cibiyar da manyan makamai.
“An ce maharan sun isa wurin ne da misalin karfe 05:20 na yammacin jiya Lahadi, inda nan take suka nufi babbar kofar inda suka yi artabu da jami’an ‘yan sanda da makamai kafin suka shiga tsakar gidan.
“Duk da cewa sun samu shiga tsakar gidan, amma duk da haka sun fada tarko a ciki, inda nan take aka Karu wasu jami’an daga Hukumomin tsaron kasar nan, domin su taimaka wa masu gadin cibiyar, domin killace katangar da ma yankin baki daya.
“A halin yanzu an shawo kan lamarin yayin da jami’an tsaro daga Hukumomin Tsaro daban-daban suka ci karfin maharan kuma Za a yi Karin bayani Nan gaba kadan”, in ji shi.