HURIWA ta caccaki Buhari kan shirun sa akan Harin Jirgin Ƙasa Kaduna
Ƙungiyar Marubuta Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Najeriya a ranar Talata ta caccaki Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari akan shirun sa akan harin da ƴan ta’adda suka kai a Filin Jirgin Saman Kaduna dana Ƙasa.
Ƙungiyar ta kuma ƙalubalanci Gwamnatin Tarayya data kasa ɗaukar matakin gaggawa akan abinda ya shafi tsaro a Ƙasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Cibiyoyin Kirkire-kirkire Na SDGs Don Bunkasa Tallafin Zaman Takewa Na Jihohi
Majiyar Jaridar The PUNCH a ranar Litinin da daddare ta bada rahoton yadda ƴan ta’adda suka tada bama-bamai akan Hanyar Jirgin Ƙasa ta Kaduna tare da kai mashi hari cike da fasinjoji.
Haka zalika, Ƴan bindiga a ranar Asabar sun kuma kai hari a Filin Jirgin Saman Kaduna. Amma har yanzu Fadar Shugaban Ƙasa har yanzu bata yi wani jawabi tana nuna rashin jindaɗi akan harin.
A cikin wata sanarwa da aka fitar Abuja, HURIWA tace “ƴan bindiga sun tada bama-bamai a Jirgin Kasa dake zuwa Abuja.
“Abun baƙin ciki ne yadda Shugaban Ƙasa bata fito ta caccaki lamarin ba, ko kuma nuna damuwa akan wannan ta’addanci.