By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Gombe ta gargadi masu shirin siyar da katin rigakafin COVID-19 dasu daina ko kuma su fuskanci hukunci.
jaridar Dimokuradiyya ta rawaito Gwamnatin ta bayyana cewa yin allurar rigakafi kyauta ne.
Da yake bayar da gargadin a ranar Alhamis a karamar hukumar Balanga, mataimakin gwamnan jihar, Dokta Manassah Jatau, ya lura cewa allurar rigakafi ita ce mafi kyawun ‘kayan aiki’ don rigakafin COVID-19.
Sannan yace, “Ya zuwa yanzu, rigakafin shine mafi kyawun kayan aiki’ don kare mutane daga cutar COVID-19, da illolin da ba a so.
“Dabarun allurar rigakafin da jihar ta dauka shine don tabbatar da fa’idarta da isa zuwa ga allurar.”