Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya shawarci gwamnatin tarayya da ta samar da makamai na zamani muddin ana so a yaƙi ta’addanci.
Tl sai dai Babangida ya ce wani hanzari ba gudu ba shine, dole ne a samar da kwararrun soji wadanda za su iya sarrafa Makaman.
Da yake tattaunawa da tashar BBC Hausa, IBB ya ce ba sau daya ba, ba biyu ba ya sha shawarta gwamnatin tarayya kan hanyoyi da kuma dabarun da za ta bi wajen dakile wannan matslaa ta tsaro dukda cewa bai fiye yawan surutu ba.
“Kwarai Kuwa Sojin Najeriya na bukatar makamai na zamani, kazalika dole ne amma a samu kwararrun soji da za su iya sarrafa makaman ba wai kawai a baiwa kura ajiyar nama ba”
Ya ce wani abin da zai kara taimakawa wajen tabbatar da kawo karshen kwamachalar tsaron shine samun hadin kai da goyon baya da yan kasa.