By Ishaq Dabai
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka ta ICPC, ta bayar da umarnin a mayar da aikin ginin wasu makarantu guda 3 a yan kunan mazabu daban daban saboda rashin ingancin ginin a Jihar kano.
Mataimakin shugaban hukumar ta ICPC na kano Bukar Galadima shine ya bayar da umarnin a yayin ziyar duba yadda ayyuka suke a mazabun ranar litinin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a yarin hukumar sun kai ziyara karamar hukumar Madobi, da Kura da kuma Garum Malam, shugaban yace makarantun furamare na Garum Malam guda 3 an kammala su amma suna da lahani sannan basu da inganci, a bisa yadda kwangilar take, a sabo da haka an baiwa dan kwangilar umarnin sake ginin.
Hukumar ta sanya ido wajen sanya sanarwa a aikin kwangilar ginin makarantun furamare ta Garum Malam, da Yadakwari da kuma Dumaji wanda dan majalissar tarayya ya dauki nauyin aikin wanda ba’ayi rufin kwano mai inganci ba a makarantar.
Kazalika sun ziyar ci Garin Dau dake karamar hukumar Warawa da kuma makarantar kimiyya ta shekarau dake Karamar hukumar Taruni wanda take karkashin Kano ta tsakiya kuma anyi aikin ginin a shekarar 2020 inda tuni an kammala aikin amma rufin makarantar yana zubar da ruwa kuma babu kujeru masu inganci da sauran kayayyakin aiki a makarantar.
A yayin gudanar da aikin Jaridar Solacebase ta rawaito cewa hukumar ta ICPC ta fitar da rahoton makarantun furamare guda 7 ranar Litinin, cewa makaranta daya ce kawai suka karfafa wacce suka samu aikinta ya kammala dake Yan Dusa a mazabar Dawakin Kudu a cewar dan kwangilar.
Shugaban tawagar Bukar Galadima yace yana gargadin ‘yan kwangilar dasu dinga kula da aikin kafin a dawo dasu baya, idan kuma ba haka ba za’a tilasta su dawo da kudin ga wanda ya dau nauyin aikin.