Hukumar kula da rage rashawa da makamantan laifuka, ICPC ta ce babu adalci a cikin rahoton da Hukumar dake sa ido kan rashawa a duniya ta Transparency International, TI ta yi.
Kakakin hukumar ta ICPC, Rasheedat Okoduwa, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Jumma’a ta ce hukumar Transparency ta kau da kai kan kokarin da gwamnati mai ci take yi na dakile rashawa a kasar.
Ta ce, daga cikin kokarin akwai maka duk wanda aka kama yana rashawa a kotu, da kuma yanke musu zama a gidan kaso, ciki har da wadanda ake musu kallon su shafaffu ne da mai.
A cewarta, a zahiri gwamnatin nan ta samar da wasu dabaru da dama don tabbatar da an fayyace komai a fili.
Ta ce, daga ciki akwai, tsarin bai daya na ma’aikatan gwamnati, IPPIS, GIFMIS, asusun bai daya na TSA da kuma wanda aka fito da shi kwanan nan www.opentreasury.