Shugaban kungiyar matasa Fulani na kasa (Fulani Youths Association), Alhaji Saudi Maikano-Adamu, ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakan farfado da makarantun al’ummar Fukani dake a fadin tarayya kasar nan. Alhaji Maikano-Adamu ya yi wannan bayanin ne a tataunawarsa da manema labarai a unguwar Mister Ali, dake kusa da Jos, a jihar Filato a jiya Laraba.
Ya yi korafin cewa a halin yanzu makarantu da tsarin ilimi na Fulani sun bace a wasu jihohin tarayya kasar nan gaba daya. Inda ya ce idan ana son tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Fulani to dole a karfafa harkar iliminsu don ilimi na taimakawa wajen inganta zamantakewar al’umma a duk inda suke. “Ilimi na daga cikin sirrin tabbatar da cigaba haka kuma ilimi na a kan gaba wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin dukkan al’umma ba
tare da nuna banbancin addini ko kabilanci ba.
Ya kara da cewa; “A kan haka ne a matsayinmu na ‘yan kungiyar ‘Jonde Jam association’ muke kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta farfado harkar ilimin yaran Fulani saboda mahimnancinsa ga zamantakewar al’umma, ” inji shi.
Shugaban kungiyar ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki su cigaba da yin yekuwar zaman lafiya a duk inda suka samu kansu, don haka ne zai tabbabatar da cigaba mai dorewa.