Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU ta sanar da cewa za ta ci gaba da yajin-aikin da take yi har sai gwamnatin tarayya ta biya mata dukkan buƙatunta.
Shugaban ƙungiyar Farfesa Biodun Ogumyemi ne ya bayyana hakan a jami’ar garin Fatakwal da ke jihar Rivers, lokacin taron masu ruwa da tsaki domin sanar da al’ummar ƙasar nan muradinsu, yana mai cewar wajibi ne gwamnantin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar cimma da suka a cikin shekarar 2012.
https://dimokuradiyya.com.ng/yajin-aiki-za-a-koma-teburin-sulhu-tsakanin-gwamnati-da-asuu/
Ya ƙara da cewa buƙatunsu na ciyar da ƙasar nan gaba ne tare da kyautata harkokin koyo da koyarwa, wanda ɗaliban jami’o’i a ƙasar nan za su ci moriyarsu matuƙar aka aiwatar.
A don haka ne ya buƙaci ɗaliban su ƙara haƙuri da halin da ake ciki a yanzu na yajin-aikin.
Farfesa Ogunyemi ya ce har yanzu malaman jami’o’in ƙasar nan na karɓar albashi ne bisa tsarin da aka d6ora su a kai na shekarar 2009, wanda hakan ya nuna cewar babu wani gyara da aka yi a kan abinda suka nema.