AbdulRaaheed Bawa shugaban hukumar EFCC ya gayama Mutanensa idan akwai mai cin hanci a cikinn su, to su gaggauta ajiye aikin su.Kamar yadda Jaridar the cable ta wallafa a shafinta
Ya fadi hakane lokacin da yake bayani a babban Ofishin su dake Makurdi babban birnin Jahar Benue, Bawa yace ana bukatar jajircewa da maida hankali wajan gudanar da aiki.
Ya cigaba da cewa babu yadda za’ayi mai cin hanci yace zaiyi fada da masu cin hanci.
KARANTA:- FG ta amince da biliyan 6.25 don kiwon shanu a Jahar Katsina
“Bari in tunama kowannanmu wannan aiki ne na musamman, wanda gwamnati, Mutanen Najeriya da sauran kasashen ketare na sanya Ido kanmu, don ganin munyi kyakykyawan aiki.”
“Ba za mu amince da duk wani nau’in cin hanci a wannan hukumar ba, ba damuwarmu bane idan munyi aiki da mutane kadan nagartattu, kuma a shirye muke mu kori duk wanda muka kama da cin hanci, idan akwai wanda yake ganin bazaiyi abunda kasa ta daukeshi yayi ba, to yana iya ajiye aikin sa.”
Ya kuma shawarci sauran ma’aikatan dasu zage damtse wajan tabbatar da aikinsu.
Kamar yadda ya fada, “hukumar ba za ta huta ba har sai ta cimma abunda kasa ta sanya su, sannan kasashen ketare sun tabbatar da cika ayyukan su.”
Yace hukumar kuma zata cigaba da kawo cigaba ga ma’aikatanta ta hanyar salon horaswa daban-daban.
“Muna cigaba da gyara, da samarwa da kuma yin kwaskwarima ga makarantun EFCC, wannan don kawai ma’aikatanmu su samu isashshen gurin aiki, don aiwatuwar aikin da aka bukacesu dayi, sannan kuma da cimma burinkan kasa a kanmu.
A wani labarin
Za ayi wadaka da man fetur da Sallah, cewar sashin dake kula da man fetur na kasa
Sashin dake kula da harkokin man fetur ta Kasa watau (DPR), sun alkarwatama Mutanen Najeriya za su wadata da man fetur a lokacin bikin babbar Sallah.
Mista Paul Osu, shugaban hulda da jama’a na cibiyar, ya bada tabbacin haka a wani bayani daya gabatar a ranar Juma’a a Legas.
Gwamnatin tarayya dai ta sanya Talata 20 ga watan July da kuma Laraba 21 ga watan July na wannan shekarar a matsayin ranakun shagulgulan Sallah.
Osun yace, da akwai man fetur sosai, ya kuma yi kira ga Yan kasuwa da kada su rinka boye man fetur da nufin kuntatawa al’umma.
Yace sashen DPR zaibi diddiqin zirga-zirgan wajan tabbatar da an samar da wadatacce kuma ingantattaccen man fetur abisa yadda dokar sashen ta tsara.
Osun, ya kuma shawarci jama’a dasu Kai rahotan duk wanda suka ga yana boye man fetur ko yana misantashi ga hukumar DPR mafi kusa dashi a fadin kasar nan.
Ya kara jawo hankalin mutane dasu cigaba da bin doka kamar yadda sashen ya tsara na yin dakon man fetur ko amfani da man fetur.
Osun ya cigaba da cewa sashen na iya kokarin sa wajan samar da hanyoyi daban-daban wanda za a samar ma masu jari da sauran Yan kasuwanni dama da hanyoyi daban-daban.