A jiya Juma’a ne wani matashi mai suna Comr Shehu Alkaleri ya wallafa wani rubutu a shafin Facebook ina jama’a da dama suka yi ta tafka muhara.
Rubutun wanda ya wallafa a shafin nan da yake tashe a Facebook mai suna “Northern Dialogue” ya janyo cece-kuce matuƙa, ciki har da wata matashiya mai Maryam Adam Usman Gagava.
Rubutn da matashin ya wallafa ya shafi batu ne na zamantakewar aure inda yake tambayar mata za su iya sany kayan da mai gidansu ya yi musu tare da yar aiki.
” Yanzu idan Mijin ki ya miki anko da yar aikin ki za ki saka” tambayar tasa kenan.
To sai dai sharhi da ya fi daukar hankali shine na mace mai suna Maryam Adam Usman Gagava, inda ta bayyana karara cewa ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa.
Cikin sharhin da Matashiyar ta yi ta bayyana cewa muddin hakan ta faru, to lallai ita ma tana da mafita, domin sau da ta sayi nata kayan ta chanchare su da mai gadi.
“Zan sa kuma zan mana anko da kai gadi, mu saka tare shi ma ya ji idan da daɗi”
Ko da yake rubutun an yi shi ne don raha, to amma jama’a da dama sun bayyana cewa a zahirin gaskiya matashiyar ta cika abin kwatance bisa irin tsaurin kalaman nata.