Idan na Zama Gwamnan Jahar Kaduna, zan ɗora daga Inda El-Rufa’i ya tsaya — Cewar Sanata Uba Sani
Sanata Mai Wakiltar Kaduna ta tsakiya Kuma Dan takarar Gwamnan jihar kaduna a Karkashin jam’iyar APC Mai Mulki Uba Sani ya bayyana cewa zai ɗora daga inda El-Rufa’i ya tsaya wajen shimfiɗa ɗumbin ayyukan cigaba a Jahar Kaduna
Sanata Uba Sani ya sanar da hakan a jiya (Asabar) a gidan Kashim Ibrahim a wani taron masu ruwa da tsaki daya wakana.
A cewar sa “ina da ƙudurin aniyar ɗaukaka Jihar Kaduna zuwa ƙololuwar mataki na gaba ta hanyar ɗorawa da gina kyawawan abubuwan da gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufai ta shimfiɗa.
“Na yi alƙawarin tafiyar da gwamnati ta fuskar kawo ci-gaban jama’a da haɗin kai a tsakanin su”. Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mustapha Inuwa ya buƙaci Masoyan sa da kada su damu da Ƙazafin da ake mashi
Uba Sani ya ƙara dacewa a halin yanzu tuni Shuwagabannin Al’umma, dana Addini, da ƴan Jam’iyya suka duƙufa wajen wayar wa Al’umma kai akan mahimman ƙudirorin da zai ɗora akan bayan ya samu nasarar zama Gwamnan Jahar.
Sanatan ya yabawa mahalarta taron da suka haɗa da tsofaffin ƴan majalisar tarayya dana Jahohi, da masu riƙe da manyan muƙamai.
A saƙon godiyar sa yace “Shugabannin ƙananan hukumomi da manyan jami’an gwamnati da shuwagabannin mata, da suka yi min rakiya zuwa kananan hukumomi 4 a ƙoƙarina na neman kujerar Gwamnan Jihar Kaduna, abun a yaba ne”.
Daga cikin waɗanda suka rufawa Sanata Uba Sani baya sun haɗa da, Hon. Abubakar Mamadi (tsohon Ɗan Majalisar Tarayya) da
(Hon Bashir Zubairu (Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna)da Hon. Aminu Shagali (Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna
Sai Hon. Ahmed Chokali (shugaban masu rinjaye, majalisar dokokin jihar Kaduna) da Hon. Yakubu Soja (tsohon Ɗan Majalisa a majalisar dokokin Jahar Kaduna
Da Kuma Hon Hayatu Usman (Tsohuwar ‘yar majalisar dokokin jihar Kaduna)
Akwai kuma Hon. Aliyu Idris (Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria)da Kabiru Jarimi ( Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu), da Hon. Abubakar Buba (Shugaban Ƙaramar Hukumar Lere) da Hon. Bashir Zuntu ( Shugaban Ƙaramar Hukumar Kubau)
Haka zalika akwai Hon. Muktar Baloni ( Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa) da Hon. Jaja (Shugaban Ƙaramar Hukumar Kudan), da kuma Hon. Abubakar Shehu (Shugaban Ƙaramar Hukumar Giwa) Da Hon. Abubakar Master (Tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Sabon Gari)
Da kuma Hon. Naziru (Mataimakin shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa).
Har ila yau akwai Arch. Sani Abbas (mamba a kwamitin shugaban kasa akan mai da iskar gas), da Injiniya Namadi Musa (tsohon Darakta-Janar na Hukumar Kula da Harkokin Addinai) da
Hajiya Rabi Salisu (Uwar Marayun Zazzau) da Hon. Ibrahim Shehu Haske (mai ruwa da tsaki na jam’iyyar a Ƙaramar Hukumar Giwa.
Sauran sun ƙunshi Dr. Fatima Zuntu (ma’aikaciyar lafiya) da Hajiya Hafsat (ƴar jam’iyya) da Salisu Ayaga (mai ruwa da tsaki, a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu ) da kuma Bala Danja (mai ruwa da tsaki na Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu ), gami da Baba Lere (mai ruwa da tsaki, a Ƙaramar Hukumar Jama’a ).
Sanata Uba sani ya kasance ɗaya daga cikin Ƴan takarar Gwamna, da yake da Mafi kwarjini da karfin tarin jama’a da mabiya.