Kungiyar Malaman jami’o’i da aka fi sani da ASUU sun ce idan har sai sun bada lambar sirrinsu ta asusun ajiyar bankinsu ta BVN ne za a biya su albashin watan Fabarairu da Maris da gwamnatin tarayya ta rike musu saboda ba su shiga tsarin IPPIS ba, to gwamnati ta ci gaba da rike albashin, domin ba za su ba da ba.
A ranar dai Talata ne shugaba Buhari ya nemi kungiyar ASUU din da ta turo da sunaye da lambar BVN na membobinta da ba su shiga tsarin IPPIS ba domin a biya su albashin watan Fabarairu da Maris saboda saukaka musu da iyalansu sakamakon cutar Korona. Kamar yadda ministan Kwadago, Dr. Chris Ngige ya tabbatar.
Dr. Ngige ya ce Malaman jami’ar za a biya su da zarar shugaban Jami’o’in sun sanya Malaman jami’ar sun bada lambar sirri ta bankinsu wato BVN.
Tun dai a ranar 23 ga watan Maris ne ASUU ta ayyana yajin aikin sai baba ta gari sakamakon kin su da tsarin IPPIS da kuma gazawar da gwamnatin tarayya ta nuna wajen cika alkawarin shekarar 2019 da aka kulla tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya.
Shugaban ASUU din, Farfesa Biodun Ogunyemi, shi ne ya tabbatarwa da manema labarai hakan a Abuja cewa ba za su bada BVN din ba.
Ya ce sun ji dadin zancen shugaban kasar, amma tun farko ma ba bukatar a rike musu albashin Fabarairu da Maris. Sannan batun sai sun bada BVN, to ba za su bayar ba, domin a baya ai an biya membobinsu ba tare da lambar BVN din ba. Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce suna zargin bada lambar BVN yana da alaka da IPPIS din da suka ki yarda da shi.