Tun barkewar cutar Kwalera a kasar nan kimanin Mutane 30 suka mutu inda sama da mutane dubu biyu ke kwance a Asibitoci daban-daban a Jihar Jigawa. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Dakta Salisu Mu’azu Sakatare na dindindin na hukumar lafiya na Jahar Jigawa ya tabbatar da wannan.
Yace kaso mafiya yawa wadanda ke dauke da cutar yara ne, a gaba daya kananan hukumomi tara da cutar tai kamari.
KARANTA:- YANZU:YANZU: Dan fafutukan kafa kasar Yarbawa Sunday Igboho, ya shiga hannu a Cotonou
Dakta Salisu Mu’azu ya lissafo wadan su garuruwa da abin yayi kamari kamar su Hadejia, Dutse, Kirikasamma, Birnin Kudu da Ringim da saura wadan su wanda kutar ta leka.
Yace Kawo yanzu dai sama da mutane dubu biyu ne suke fama da cutar, wadansu suna kwance a Asibitocin gwamnati daban-daban wasu kuma sun gidajen su.
Sakataren bai dai ce ga musabbabin aukuwar lamarin ba, sai dai yafi dangata lalurar barkewar cutar Kwalera a Hadejia da rashi ruwa mai kyau.
Da yiwuwar akwai wani yanki da har yanzu suna bayangida a waje kuma ruwa na biyowa ta wajejen.
Dakta Salisu Mu’azu yace gwamnatin Jahar na iya bakin kokarin ta don ganin ta shawo kan matsalar.
Sakataren hukumar ta lafiya na Jigawa yace hukumar da take tallafawa kananan yara watau UNICEF, ta aiko da Magunguna da dama, ta kuma yi alkwarin sake aiko da wadansu da dama.