Wata kotun gwamnatin tarayya dake Jos a ranar Talata ta bai wa Babban Sufeto Janar na ‘yan Sanda, da kuma mataimakin Kwamishina, Abba Kari mai kula da sashen ba da tallafin gaggawa na tsaro da su gabatar da wani da ake zargi a raye ko a mace.
Mai Shari’a Dorcas Agishi Kotun ta 1, ita ce ta ba da wannan umurnin a wani korafi guda biyu da D.G. Dashe, ya shigar gabanta. Sai dai Lauyan da ke tsayawa wanda ake zargi, Nanpon Sambo, ya yi zargin cewa wanda yake karewan ya mutu a wurin ‘yan Sanda a Abuja.
Mai shari’ar ya bai wa ‘yan sanda mako biyu domin su gabatar da wanda ake zargin, ko kuma su fuskanci hukunci daidai da doka da tanadar.
Rahotanni sun bayyana cewa; a ranar 25 ga watan Satumba ne, Dashe ya shigar da kara biyu wanda ya nemi kotun da ta bai wa Sufeto Janar na ‘yan sanda umurnin su gurfanar da Sambo wanda yake fuskantar shari’a bisa zargin rike makamai ba bisa ka’ida ba.
Wannan korafin ya biyo baya ne, bayan da Lauyan da ke kare ‘yan sanda Joshua Ayanna a cikin watan Yuli, wanda ake zargin ya mutu a wurin ‘yan sanda.