Odion Ighalo yana fatan za a tsawaita zaman aron da yake yi a Manchester United har zuwa karshen Gasar Premier ta bana.
Dan wasan na Najeriya, mai shekara 30, ya koma United daga Shanghai Shenhua ta kasar China a watan Janairu kuma kwantaraginsa zai kare ranar 31 ga watan Mayu.
Shugabannin Gasar Premier suna fatan za a ci gaba da kakar wasa ta bana a watan Yuni, yayin da ake sa ran ci gaba da gasar League ta China nan ba da jimawa ba, abin da zai sa Ighalo ya koma Shanghai.
Ighalo ya shaida wa BBC Sport cewa: “Ina son kammala kakar wasa ta bana idan da hali”.
“Ina cike da kuzari, inda nake zura kwallaye amma yanzu an tsayar da komai fiye da wata guda. Na yi bamkin kokarina kuma ina fatan za mu koma fagen tamaula”.
“Kungiyar tana kan ganiyarta kafin barkewar annobar
[korona]
. A halin da ake ciki ina zaman aro ne, don haka lokacina a kungiyar a takaice yake.”
BBC Sport ta fahimci cewa United tana son tsawaita kwangilar Ighalo.
Ya zura kwallo hudu a wasa takwas da ya buga wa United a dukkan gasar da suka yi, ciki har kwallo guda da ya zura a wasan da suka doke LASK da ci 5-0 a Europa League ranar 12 ga watan Maris, kwana guda kafin a dakatar da gasar Premier.