Daga: Uzairu Lawal Rigasa
Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya koka kan yadda wasu masu shirya fina-finai da masu sana’ar skit dake sayar da kayan ‘yan sanda ba tare da izini ba.
IGP din ya kuma bayar da umarnin kamawa tare da gurfanar da ’yan wasan kwaikwayo da masu yin skit kan mallakar kakin ‘yan sanda ba tare da izini ba kuma ba bisa ka’ida ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Wike Ya Gana Da Gwamnoni Da Masu Ruwa Da Tsaki Na Jam’yyar A Abuja
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana damuwarta kan yadda wasu mutane,masu shirya fina-finai da masu sana’ar siyar da kayan kwalliyar ‘yan sanda ke yi ba bisa ka’ida ba tare da yin amfani da kakin ‘yan sanda ba tare da izini ba, da kuma yadda ‘yan kasuwa ke siyar da kayan ‘yan sanda ba bisa ka’ida ba a shaguna.”
“Buɗaɗɗun shagunan da hukumar ‘yan sanda ba ta amince da su ba.”
“Hakazalika, IGP din ya fusata kan yadda masu shirya fina-finai da masu yin fim ke nuna hukumar ‘yan sanda a cikin fina-finansu da skits, suna amfani da kakin ‘yan sanda ba tare da la’akari da tanadin sashe na 251 na dokar manyan laifuka ba, da sashe na 133 na hukumar.”
“Dokar Penal Code wacce ke haramta irin wannan amfani mara izini tare da rakiyar takunkumin da ya dace.”
“Saboda haka IGP ya tuhumi duk wani tsari, IGP Monitoring Unit, Provost marshals da X-Squad, da su kama su kuma gurfanar da su nan take.”
“Kamar yadda doka ta tanada, duk wani mutum ko gungun mutanen da ke da hannu wajen siyar da kakin ‘yan sanda ba bisa ka’ida ba. a cikin hukunce-hukuncen su, yayin da masu yin fim ko skit da ke nuna jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya a cikin mummunan yanayi, ba tare da neman izini ba, ko kuma an ba su takardar izini ga irin wadannan hotunan, da su daina nan take ko kuma su fuskanci fushin doka.”