Babban Sufeto Janar na ’yan sanda kasar nan, Mista Usman Baba ya umarci kwamishinonin ‘yan sanda a duk fadin kasar nan da su fara aiki da kwamitocin tuntuba tsakanin hukumomin da ke kula da harkokin zabe.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar , CSP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Baba ya ce, an ba da umarnin a sanya masu ruwa da tsaki wajen samar da dabarun dakile barazanar da ake tunanin fuskanta a babban zaben 2023.
Ya ce tashe-tashen hankula na siyasa, kalaman nuna kiyayya, barazana, rashin aminci da siyasa, rashin fahimtar juna da tsattsauran ra’ayi na siyasa, na iya zama barazana ga dimokradiyya da tsaron kasa.
KARANTA KUMA IGP: Za Mu Samar Da Ofisoshin Yan Sanda Na Zamani A Fadin Kasar Nan
Don haka, IG, ya umurci kwamishinonin da su yi aiki tare da dukkan membobin kwamitin don magance barazanar rikice-rikice na siyasa da kuma tabbatar da gaggauta gurfanar da masu karya dokokin zabe.
Ya kuma umurci kwamishinonin da su tabbatar da isassun jami’ai da kororinsu bisa dabaru, tare da hada kai da sa ido daga dukkan jami’an tsaro da aka tura domin gudanar da zaben.
Baba ya ce matakin ya zama dole domin karfafa dukkan cibiyoyin hukumar zabe ta kasa (INEC) da suka hada da kayan zabe.
Ya kuma ce an yi hakan ne domin tabbatar da tsaro da tsaron ma’aikatan hukumar zabe da kayan aiki kafin babban zabe da lokacin da kuma bayan babban zabe.
Hakazalika, IG ya ba da umarnin rarraba sabbin na’urori, kayan yaki da tarzoma, da kayan kariya ga ‘yan sanda a duk fadin kasar don shirye-shiryen zaben.
Ya kuma jaddada aniyar rundunar ‘yan sanda na kare al’amuran dimokradiyya da tsaron kasa.
Baba ya bukaci daukacin mambobin kwamitin tsaro na zaben da sauran jama’a da su taimaka wajen tabbatar da tsaro da tsaron kayayyakin zabe, ma’aikata da masu kada kuri’a kafin zaben 2023, lokacin da kuma bayan zaben. (NAN)
A Wani Labarin Kuma Shugabannin Afrika Sun Yabawa Buhari Bisa Kyakkyawan Shugabancinsa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cikin wannan mako, ya lashe zukatan ’yan uwansa shugabannin Afirka a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, inda suka yi ta ba da shaida masu kyau na halayen shugabancinsa.
Majiyar Dimokuradiyya ta bayar da rahoton cewa, shugabannin kasashen Afirka sun je birnin Yamai ne domin halartar taron kolin bunkasa masana’antu da habaka tattalin arzikin kasashen Afirka, da kuma wani zama na musamman kan yankin ciniki cikin ‘yanci na nahiyar Afirka (AfCFTA).