Masu amfani da shafukan sada zumunta sun mayar da martani sosai kan faifan bidiyon wata sabuwar uwa da ta ki taba jaririn ta inda ya jawo cece-kuce, Legit.ng ta rawaito.
A cikin wani faifan bidiyo mai ban tausayi, wata ma’aikaciyar jinya ta mika mata jaririn a asibiti amma ta ki taba jaririn nata
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda Wata Tsohuwa Ta Haifo Santaleliyar Jaririya Tana Da Shekaru 71 Bidiyon Ya Dauki Hankali
Duk da kokarin da ma’aikaciyar jinya ta yi na ganin ta dauki jaririn nata, matar ta ki, har ma ta kau da kai
Sabuwar uwa ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ta ki taba ko daukar sabon jaririn da ta haifa.
A cikin faifan bidiyo mai raɗaɗi da aka gani akan TikTok, wata ma’aikaciyar jinya ta kawo jaririn ga sabuwar mahaifiyar da ke zaune a cikin keken guragu.
Da ganin yaron nata, sai fuskar matar ta cika da bakin ciki yayin da ta yi wa ma’aikaciyar jinya alamar ta tafi da yaron.
Sai dai ma’aikaciyar jinya ta yi murmushi ta ci gaba da kawo mata jaririn. Tana mayar da martani sabuwa uwa tayi saurin juyar da fuskarta zuwa wani wajen.
Rikici iri-iri sun biyo bayan faifan bidiyon kamar yadda wasu ke ikirarin cewa ciwon ciki ne bayan haihuwa, yayin da wasu suka yi tir da matakin da matar ta dauka.
A wani labarin kuma, Oba Na Benin Ya Tunbuke Rawanin Wani Basaraken Gargajiya
Sarkin Benin, Oba Ewuare II, ya kori Mista Edomwonyi Iduozee Ogiegbaen a matsayin Enogie na Egbaen Siluko a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabas ta jihar Edo.
Korar Ogiegbaen ta zo ne bayan an tsige shi a matsayin babban ko-odinetan fada a kan al’amuran Enigie a watan Janairu, 2023, bisa zargin tawaye, rashin aiki da kuma tayar da zaune tsaye a Enigie fold a Masarautar Benin.