By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a matsayin wani “musibi da bala’i” da aka bayar da rahoton mutuwar dubunnan mutane a daren Juma’a bayan da wata haramtacciyar matatar mai ta fashe a dajin Abaezi da ke karamar hukumar Ohaji-Egbema a jihar Imo.
Shugaban kasar, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya umurci sojojin kasar da jami’an tsaro da na leken asiri da su kara kaimi wajen dakile ayyukan matatun mai ba bisa ka’ida ba.
Shugaba Buhari ya ce alhakin asarar rayuka da dukiyoyi dole ne ya kasance ga masu daukar nauyin matatar ta haramtacciyar hanya, “wadanda dole ne a kama su kuma a hukunta su.”
Ya mika sakon ta’aziyyar da kuma cikakken zurfin firgici da tashin hankali na kasar ga iyalan wadanda abin ya shafa, al’ummar Ohaji Egbema da gwamnati da mutanen jihar Imo.
Shugaban ya bukaci shugabannin al’umma, ’yan sanda, da ma’aikatan sirri da kada su sake barin faruwar lamarin mai ratsa zuciya a wani yanki na kasar nan gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan afkuwar hatsarin ne dai a ranar Asabar kwamishinan albarkatun man fetur na jihar, Goodluck Opiah, wanda ya yi magana a madadin gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo a ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru, ya ce gobarar ta lashe rayukan dimbin matasa.
Kimanin wasu 150 kuma, a cewar rahotannin da suka ganewa idanunsu, sun samu mummunar konewa.
Comments 1