Wani matashi mazaunin kasar Sudan ya bayyana yadda tsananin zafin rana ke addabar su a kasar, inda har ta kai ga ya nuna wa mutane cewa gani ya kori Ji.
Cikin wani faifan bidiyo da ya watsa a shafukan sada zumunta na zamani, matashin ya nuna wa jama’a ƙarara yadda zafin ranar ta kai ga har yana soya kwai.
A yanayi na ban mamaki, matashin ya sanya yar tukunyar soya kwan a tsakar rana, inda nan da nan ya fasa kwan ya juye shi cikin tukunyar, kuma ba tare da ɓata lokaci ba kwan ya soyi cikin dakikoki.
To sai dai jama’a da dama na nuna shakkun su kan wannan al’amari, inda wasu ke ganin akwai wani siddabaru a cikinsa.