Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya yi zargin ƙungiyar Boko Haram da ci gaba ɗaukar mutane su taya su yaƙi, ciki har da waɗanda suka tilasta wa zama ‘yan gudun hijira.
Gwamnan ya alaƙanta hakan da rashin samun abin da jama’ar ke buƙata a sansanonin gudun hijrar, musamman damar komawa garuruwansu domin su ci gaba da noma da sauran sana’o’in da su ka saba.
“Gaskiya ne ƙungiyar Boko Haram na ribatar mutane domin su shiga cikinta kuma hakan kuma abin tsaro ne” cewar gwamna Zulum.
A hirarsa da Sashen Hausa na BBC, ya ƙara da cewa: “Mutane sun gaji da zama a sansanin masu hijra, ba su samun abin da suke so.
“Dole ne su koma garuruwansu domin samun damar yin noma da kiwo kasancewar babu wata gwamnati da za ta iya samar da ciyarwa gare su mai ɗorewa”.
Gwamnan wanda ya ce sun samu nasarar mayar da mutane garuruwan Kukawa da Mafa sannan nan gaba “za mu mayar da mutanen Kawuri.”
“Amma muna fatan sojoji za su ƙara ƙaimi wajen ganin an mayar da al’ummar Baga da Marte da Malam Fatori da Guzamala,” cewa gwamZulum.