Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
Daya daga cikin jarumai mata a masana’antar fina-finai ta Kannywood Jaruma Sadiya Adamu, ta nuna godiyar ta ga Allah bisa Nasarorin da ta samu a cikin masana’antar, wanda ta bayyana su da cewar suna da yawan da ba za su lissafu ba.
Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Dimukaradiyya da ya ke yi mata tambaya dangane da irin nasarar da ta samu a cikin harkar fim, in da ta ke cewa.
“Na samu Nasarori da dama kuma ina alfahari da hakan, saboda na samu abubuwa ta dalilin harkar fim, tunda ga ni ina cikin rayuwa ta rufin asiri babu abin da ya fi karfi na za ka taimaka wa jama’a da sauran masu neman taimako. Ka ga wannan shi ma rufin asiri ne. ”
KARANTA WANNAN LABARIN: An harbe wani Makiyayi Dan shekara 18 a Filato
Dangane da irin Matsalolin da ta samu kuwa. Sadiya Adamu da ce” Gaskiya ban samu wani Kalubale a cikin harkar fim ba. A lokacin da zan fara da na zo na fada a gidan mu suka ki yarda har kuma Allah ya sa, da yake ina da rabo nan kuma hanyar cin abinci na take suka amince da na yi. Kuka tun da na shigo harkar ban hadu da kowacce irin matsala ba sai dai na yi nasara. “