Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajanta wa iyalan mutanen da hare-haren Boko Haram ya rutsa da su a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Shugaban ya bayyana haka cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar, inda ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da fatattakar masu ta da kayarbayan har sai an ga bayansu.
Ya kuma ce Boko Haram ”ta kusa zuwa karshe saboda dakaru na ci gaba da samun kayan aikin yaki da masu ta da tarzoma.”
A cewarsa, ”gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin tabbatar da tsaron rayukan ‘yan Najeriya, sannan hankalinta ba zai karkata ba saboda hare-haren da Boko Haram suke kai wa kan mutanen da ba su ji ba su gani ba.”