Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan wani shugaban addinin kirista a arewacin Nijeriya.
‘Yan bindiga da ake tunanin masu da’awar kishin musulunci ne sun sace Reverend Lawan Andimi a farkon watan Janairu.
Cikin wata sanarwa, shugaban kasar ya bayyana kisan Reverend Andimi a matsayin wani abu da aka yi da gangan.
Ya kuma bayyana cewa masu garkuwar sun nuna alamun za su sake shi ta hanyar mika shi hannun wasu mutane.
Sai dai ba su bayyana ko su wanene mutanen ba.
Bbc Hausa sun labarto cewa Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi tur da kisan inda kuma ta bukaci hukumomi su kara kaimi wajen kubutar da mutanen da Boko Haram ta yi garkuwa da su.
Kisan Reverend Andimi shi ne harin baya-bayan nan da masu da’awar kishin Musulunci a yankin suka kai kan mabiya addinin kirista.
A watan Disamba ne masu ikirarin jihadi da ke da alaka da kungiyar IS suka fitar da wani hoton bidiyo da ke nuna yadda suka kashe kiristoci 11 a arewa maso gabashin Najeriya.