Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya tabbatarwa da Bilgate cewar ba zai taba baiwa Al’ummar Najeriya kunya ba.
Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da mai kudin duniya Bilgate, Attajiri Bilgate, ya kira shugaban kasa Muhammad Buhari, don taya shi murnar sake lashe zabe karo na biyu.
Muhammad Buhari, yace Al’ummar Najeriya zasu yi alfahari da Gwamnatin sa koda bayan baya nan, yace yana mai Alfahari da yadda Bilgate yake baiwa Al’ummar Najeriya dama Afurka baki daya tallafi musamman ta fuskar Foliyo da cutar HIV.
Billgate, yace yana mai Alfahari tare da jin dadin kasancewa da shugaban kasa Muhammad Buhari, yayi kuma Alkawari ci gaba da baiwa Najeriya tallafin daya dace domin ciyar da kasar gaba.
Muhammad Bubari daga karshe, ya yabawa Billgate kan yadda yake zuba dukiyar sa ta bangaren ciyar da Najeriya gaba.