Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce ya fi imanin kungiyarsa za ta lashe gasar Premier duk da rashin nasarar da suka yi da Manchester City da ci 3-1 a daren Laraba. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
City ce ta fara zura kwallo a ragar Arsenal ta hannun Kevin De Bruyne, amma Bukayo Saka ya rama kwallon da bugun fenareti.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba mu ajiye wa wani yanki shugaban kasa — Dattawan Arewa
Jack Grealish ne ya saka zakarun a gaba, kafin Erling Haaland ya kara kwallo ta uku da taimakon De Bruyne.
Arteta ya dage cewa Arsenal ta “daidaita”City kuma ta yi gaba da su.
“Su ne mafi kyawun kungiya a duniya kuma muna matakin daya ne da su a yanzu.
“Ina da imani cewa (za mu lashe gasar) saboda ina ganin ƙungiyar da ke tafiya gaf da gaf tare da su,” Arteta ya shaida wa BBC Sport
A wani labari kuma, Ba mu ajiye wa wani yanki shugaban kasa — Dattawan Arewa
Kungiyar dattawan Arewa NEF, ta bayyana cewa yankin arewacin kasar bai tanadi shugabancin kasa ga wasu yankuna a zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a wajen taron dattawan Arewa da aka yi a Abuja, ya yi ikirarin cewa har yanzu Arewa na da sauran shekaru hudu da za ta yi mulki domin daidaita kudancin Najeriya