Limamin Jam’iyyar APC ta Kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce yana da yakini a ran shi cewa kasar na za ta fita daga halin matsalar tsaro dake damun ta.
Da yake magana a gurin tatin Tafsiri a Lagos House dake birnin Ikko, Tinubu ya ce ko shakka babu yan Najeriya za su sharbi romon zaman lafiya karkashin mulkin shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hau karagar mulki ne a shekara ta 2015 bisa tanadin alkawura uku da suka hada da kawo karshen Matsalar tsaro da ta Tattalin Arziki da kuma matslar makamashi.
To sai dai kimanin shekara shida kenan bayan shugaban kasar ya kakabe Jam’iyyar PDP da ta shafe shekara 16 tana, al’amurra tamkar kara rikicewa yake.
Amma Tinubu wanda aje alakanta shi da shugabancin kasar nan a shekara ta 2023 ya ce yana da yakini komai zai dawo dai-dai a kasar nan karkashin mulkin Jam’iyyar tasu.
Ya kara da cewa ya yi amann shugaba Buhari da kansa lamarin na ci Mishi tuwo a kwarya.
Daga bisani kuma ya ce uwa uba kana ummulhaba’isin wannan lamari shine yadda wasu ke siyasantar da shi don cimma wani muradin na kashin kai