Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta a matsayin muhimmiyar hanyar warware rikicinta da Isra’ila. Inda ya jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan kafa kasar Falastinu.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabinsa a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda shugaban ya tabo batutuwa da dama da suka hada da matsalar tsaro da yadda masu tsatsauran ra’ayi ke amfani da kafofin sada zumunta suna aikata laifuka da yaki da cin hanci da rashawa da muhimmancin bada ilimi da kuma tallafa wa marasa karfi.