Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya fito fili ya bayyana goyon bayan sa ga kudirin shugaban kasa na jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a dandalin Murtala da ke Kaduna inda jagoran jam’iyyar APC na kasa tare da rakiyar tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, da tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribado da sauran manyan baki suka kai wa wakilai jihar ziyarar neman goyon baya.
A baya Shetimma ya tabbatar wa wakilan cewa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yana nan tare da su.
Sai dai da yake magana El-Rufai ya ce zai bukaci goyon bayan wakilai daga jihar Kaduna domin marawa Tinubu baya.
“Ina so in yi wa Kashim Shettima gyara, saboda ya ce gwamnan yana tare da su,” in ji El-Rufai, ya kara da cewa ba zai iya zama cikakken masoyin Tinubu ba sai wakilan jihar sun amince.
“Kafin mu tabbatar da abin da Kashim Shetima ya fada a nan, ina so in tabbatar daga wakilan mu masu darajar cewa kuna tare da Asiwaju?” El-Rufai ya tambaya, wakilan suka amsa gaba daya suna ihun eh.
“Mai girma, ina yin abin da suka ce mini, su ne shugabannina. Haka APC a Kaduna ke aiki,” inji shi.
A wani labarin Kuma na daban.
Shugaban Jam’iyyar APC a jihar Bayelsa Dennis Otiotio, ya ce tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan har yanzu ba dan Jam’iyyar su bane a jihar.
Dennis ya bayyana hakan ne yayin Wata ganawa da aka yi da shi ta wayar tarihi, a safiyar yau Alhamis.
Ya kara da cewa Jonathan zai iya zamadan jam’iyyar ne idan har ya tabatarwar da duniya hakan, kuma aka samu shugaban Jam’iyyar na kasa Adamu Abdullahi shima ya tabbatar da hakan.
Otiotio na wannan jawabi ne dai dai lokaci da labarin cewa Jonathan ya koma APC ke ci gaba da zagaye Najeriya, wanda a cewar sa hakan ba gaskiya bane.
To sai dai ya ce suna maraba da kudirin Jonathan din, idan har ya kai ga yanke shawarar Komawa jam’iyya mai mulki.
Har yanzu dai ana ci gaba da cece kuce kan gaskiyar komawar Goodluck Jonathan jami’iyyar APC.
Comments 1