Fitaccen Ɗan Wasan Ƙwallon Ƙungiyar Manchester United Cristiano Ronaldo yace yana jin cewa shekarun sa 30, wanda a cewar sa akwai yiwuwar zai cigaba da wasan ƙwallon ƙafa bayan shekaru 40.
Yace da irin yadda ya baiwa jikinsa fifiko, yace yana bada mahimmanci ga lafiyar sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: COVID-19: Najeriya Ta Ba Da Rahoton Bata Samu Mutuwar Mutane Ba, Tana Da 423 Masu Dauke Da Cutar
Ɗan shekaru 36 dan asalin ƙasar Portugal, yace abinda yake fuskanta shine matsalar ƙwaƙwalwa.
“Inaji a jikina cewa shekaru na 30. Ina kula da jikina sosai da zuciya ta. Abinda na lura a lokutta da suka wuce shine bayan shekaru 33, na lura cewa zan iya yin wasa sosai.
Comments 1