Naji Tausayin Najeriya, duk da mai hura ƙwallon baya goyon bayan mu — Cewar Kocin Ghana, Otto Addo
Kocin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasar Ghana Otto Addo, yace yaji tausayin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Super Eagles ta Najeriya, domin sunyi ƙoƙari a dukkanin wasannin guda biyu da aka gudanar a wasan samun tikitin shiga Gasar Wasan Ƙwallon Ƙafa ta Duniya ta 2022 a Abuja a ranar Talata.
Addo yace mai hura Ƙwallon Ƙafa na wasan yafi son Najeriya fiye da Ƙungiyar Ƙwallon tasu ta Black Stars a lokacin wasan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wannan Kashe-kashen duk yunƙuri ne na hana Ƴan Kudu Siyasa a matakin Tarayya — Inji Ehilebo na PDP
Ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi akan nasarar da Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa tasu tashi a gasar shiga wasan Ƙwallon Ƙafa ta Duniya ta Shekarar 2022 a Qatar a wannan Shekarar.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar Najeriya tayi wasa daci 1 da 1 a filin wasan Ƙwallon Ƙafa na MKO Abiola a Abuja, biyo bayan cin da Thomas Partey yayi, da kuma na William Troost-Ekong.
Sun samu nasara sakamakon ƙwallon da aka ci a gida Najeriya, bayan tashi babu ci a wasan da aka gabatar a Kuma su na Ƙasar Ghana a ranar Juma’a.
“idan kaga damar maki, Amma Ƴan Najeriya suna da kyau,” Addo ya gayawa Magoya bayan Ƴan Wasan Ghana.
“Naji tausayin ƴan Najeriya, wannan shine Wasan Ƙwallon Ƙafa a wani lokaci, mun dai samu nasarar mu. Rafarin baya bayan mu.