Wani dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin mika mulki ga matasa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasar.
Ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin kungiyoyin sama da 200 da kuma shugabannin TeeCom dake fadin kasar nan a Abuja, kamar yadda wata sanarwar manema labarai da Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Magoya bayan Atiku, Dr Victor Moses ya sanya wa hannu.
Sanarwar mai taken, ‘Atiku don kara hada kai da matasa da kuma mika mulki ga matasa inji kungiyar ta Atiku Support Organisation’.
Atiku ya bayyana jin dadinsa yadda a yanzu haka matasa da dama ke shiga harkokin siyasa, inda ya kara da cewa zai ja hankalin matasa tare da mika musu tsarin siyasar sa domin samun nasara
An jiyo tsohon mataimakin shugaban kasar yana cewa, “Zan kasance abun kwaikwayon ku, Kuma zan mika maku mulki.
“Ina so in kara yin aiki tare da matasa saboda matasa sun fi kwarewa, kirkire-kirkire, da tattaunawa tare Samar da damarmaki da kuma magance kalubalen zamani.
“Gwamnatinmu za ta zama wata Jigo wajan mika mulki daga Dattijai zuwa ga matasa.”
Kazalika a cikin sanarwar Kungiyar goyon bayan Atiku, ta bukaci matasa da su marawa Atiku baya, tana mai cewa za su kara samun dama a karkashin mulkisa idan yayi nasara.